Dan Siyasa Ya Goyi Bayan Ganduje, Ya Ce Shi Ya Fi Dacewa da Shugabancin Jamiyyar APC

September 2024 · 3 minute read

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - A wurin Atiku Abubakar Isah, babu wanda ya fi dacewa da jagorantar jam’iyyar APC irin Abdullahi Umar Ganduje.

Atiku Abubakar Isah yana ganin Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana da duk abin da ake bukata wajen zama shugaban APC na kasa.

Kara karanta wannan

Mai son takara a NNPP ya zargi Kwankwaso da 'cinye' masa kudi lokacin zaben 2023

Atiku ya yabi shugaban APC, Ganduje

A wata zantawa ta musamman da ya yi da Legit Hausa a ranar Lahadin nan, ‘dan siyasar ya yabi tsohon gwamnan na jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya zo a lokacin da wasu suka huro wuta, suna neman ganin bayan Abdullahi Ganduje.

Atiku Abubakar matashin ‘dan siyasa ne da aka buga da su a tsohuwar ANPP har zuwa APC, kuma ya nemi takara har a NNPP.

Meyasa Ganduje ya yi zarra a APC?

Idan ana zancen ilmi, sanin aiki da gogewa, Atiku Abubakar yana ganin Abdullahi Ganduje ya yi zarra a jam’iyyarsa ta APC mai mulki.

Legit Hausa ta tambayi Atiku ra’ayinsa game da masu ganin ya kamata shugaban APC ya fito daga yankinsa na Arewa maso tsakiya.

Shi yana ganin Ganduje ya fi ‘yan siyasar yankinsa dacewa da mukamin musamman tsohon gwamnan jihar Kogi watau Yahaya Bello.

Kara karanta wannan

Wike v Fubara, Ganduje v Abba da wasu manyan gwabzawar da ake jira a 2027

Sannan Atiku yana ganin ba wannan ne karon farko da aka dauke shugabancin APC daga wani yanki, aka maida shi wani wuri ba.

Ganduje ko Yahaya Bello a APC?

“Babu ranar gama shari’a da Bello, domin zuwa lokacin Abdullahi Ganduje ya bar kujerar.”"Yahaya Bello yana wasan kura tsakaninsa da EFCC, ta ina zai zama shugaban jam’iyya?"Idan ya gama cin lokacin tsohon shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Adamu, daga nan sai a yi zaben sabon shugaban jam’iyya na kasa."

- Atiku Abubakar

Atiku ya taso Kwankwaso a gaba

Kafin yanzu kun samu labari cewa Atiku Abubakar ya ce an yi masa alkawarin samun takara, a karshe ya sa ya ji kunya a jam’iyyar NNPP.

‘Dan siyasar ya ce ya bata lokaci a banza bayan alakar da ke tsakaninsa da Rabiu Kwankwaso wanda asali saboda shi ya bi kayan marmari.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllboByfZRmm5qmXai2uq3SmmSymV2cvLq1jJuYspmeYrSiusOuoZ5lqZZ6pLGMrJ%2BiZamWeqe1jJ2YnJ2nlnqlrYysn66fkZeur6%2FIp2SjmZ2exrqt0WaYqZtf